KASUWAR HANNUN JARI: A TSARIN TATTALIN ARZIƘIN BAHAUSHE

Kira ga dukkan Hausawa masu son gina arziƙi na halak wanda zai amfane su da iyalansu

Koyi Yadda Za Ka Fara Siyan Hannun Jari a Manyan Kamfanoni da Kanka, Cikin Harshen Hausa — Ba tare da Tsoron Faɗawa Hannun 'Yan Damfara Ba!

Wannan littafin shi ne zai zame maka 'wuƙar ƙugu' a kasuwar hannun jari, wadda da ita za ka yi amfani wajen yanko riba a duk kamfanin da ka sayi hannun jarinsa, ko da kuwa ba ka da ilimin hada-hadar kuɗi a baya.

Mafita da Fa'idoji

To amma me zai faru idan aka ce ka samu jagoranci da zai nuna maka yadda ake karanta bayanai game da kamfanoni, da fahimtar irin kasuwancin da suke yi domin yanke hukunci da kanka cewa ya kamata ka siya ko kar ka siya, da kuma samun ilimi kan yadda ma ake sayan hannun jarin kamfani?

Wannan dalilin ya sa muka rubuta littafin KASUWAR HANNUN JARI: A TSARIN TATTALIN ARZIƘIN BAHAUSHE. Mun rubuta komai a cikin harshen Hausa domin ka fi fahimtar karatun da kyau.

Abubuwan Da Za Ka Koya Da Kuma Amfana Da Su:

Me Kake Jira?

Danna mahaɗin da ke ƙasa domin yin pre-order na littafin (PDF) a kan farashin rangwame na Naira 5,000 kafin lokaci ya ƙure!

Game Da Marubutan

Mujahid Muhammad Manga

Mujahid Muhammad Manga ƙwararren masani ne kuma mai koyar da kasuwancin hannun jari. Ya yi karatun digiri a fannin Injiniyanci (Civil & Water Resources Engineering) a Jami'ar Maiduguri. A ƙarƙashin shirinsa na Stock Market Master Course (SMMC), ya horar da ɗaruruwan mutane ilimin kasuwar hannun jari a Arewacin Najeriya a harshen Hausa.

Habib Sani Galadima

Habib Sani Galadima masanin harshen Hausa ne, ƙwararren mai aikin fassara, kuma ɗan kasuwar hannun jari (investor). Ya mallaki shaidar karatu ta N.C.E a Harshen Hausa daga Yusuf Maitama Sule Federal University, Kano, gami da digiri biyu (B.A. da B.Sc.) a fannin Aikin Jarida da Yaɗa Labarai daga Jami'ar Chandigarh ta Indiya da kuma NOUN. Ya taɓa zama Mataimakin Edita a jaridar The Citizen Reports. Ya fassara litattafai na ilimin tattalin arziƙi da dama ciki har da 'The Manual Money', kuma yana ɗaya daga cikin zakarun gasar rubutu ta Aminiya-Trust a shekarar 2020.

KASUWAR HANNUN JARI: A TSARIN TATTALIN ARZIƘIN BAHAUSHE

Pre-Order

Kasuwar Hannun Jari

₦5,000 — Farashin Pre-Order (Rangwame)
📖 Littafi 🎬 Bidiyon Koyarwa 📚 Ƙamus

Bayananku — Your Details

Da fatan za a cike dukkan filayen da aka buƙata.